IQNA

An Buga Tare Da Yada Wani Littafi Kan Matsalolin Matasa A Turkiya

15:49 - September 29, 2009
Lambar Labari: 1831606
Bangaren kasa da kasa; An buga tare da yada wani littafi dangane da matsalolin matasa a kasar Turkiya, wanda ya yi bayani kan irin wadannan matsaloli filla-filla.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin resalhaber cewa; An buga tare da yada wani littafi dangane da matsalolin matasa a kasar Turkiya, wanda ya yi bayani kan irin wadannan matsaloli filla-filla. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan littafi zai taimaka matuka wajen wayar da kan matasa dangane da yadda suke kallon rayuwa da kuma irin matsalolin da suke fuskanta a cikin rayuwa ta zamantakewa da kuma rayuwa ta yau da kullum, kuma littafin ya ginu a kan mahanga ta addinin musulunci. 470829
captcha