Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga jaridar Iqtsadiyya ta kasar Saudiyya cewa; Wani masani kan harkokin addini a kasar saudiyya Abdullah Ben Saleh ya yi kira da a kafa wata babbar cibiya ta kiyaye ilmomin addinin Musulunci a birnin Kirawan na kasar Tunisia. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan kira ya zo ne a dadai lokacin da malamai suke hankron dawo da martabar birnin ta fuskacin ilmi, wanda kuma birnin yana cikin biranan kasashen Afirka da ma na larabawa da suka shahara wajen yada harkokin ilmin adddinin muslunci a matsayi na duniya. 471918