IQNA

An Fara Gudanar Da Tattaunawar Addinai A Kasar Switzerland

11:48 - October 01, 2009
Lambar Labari: 1832124
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da zaman taron mabya addinai a kasar Switzerland, wanda zai mayar da hankali kan muhimman batutuwa da suka danganci sulhu da fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya a ddinai.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga jaridar kasa da kasa ta shark alausat cewa; An fara gudanar da zaman taron mabya addinai a kasar Switzerland, wanda zai mayar da hankali kan muhimman batutuwa da suka danganci sulhu da fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya a ddinai. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro an bude shi ne tare da halartar manyan baki, da suka hada da shugaban kasar ta Switzerland Hans Rodolf da kuma wasu daga cikin ministocinsa. Taron dai yana mayar da hankali kan batun sulhu da samar da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai a fadin duniya. 471956


captcha