IQNA

Za A Gudanar Da Taron Tunawa Da Shahadar Imam Sadiq (AS) A London

11:48 - October 01, 2009
Lambar Labari: 1832125
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da taron tunawa da shahadar imam (AS) a birnin London na kasar Birtaniya, wanda mabiya mazhabar shi'a na kasar Birtaniya suka shirya gudanarwa a cikin mako mai kamawa.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na IC-EL cewa; Za a gudanar da taron tunawa da shahadar imam (AS) a birnin London na kasar Birtaniya, wanda mabiya mazhabar shi'a na kasar Birtaniya suka shirya gudanarwa a cikin mako mai kamawa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daya daga cikin ierin shirye-shirye da mabiya mazhabar shi'a ke gabatarwa a kasar Birtaniya. Sheikh Ahmad Hanif ne zai gabatar da jawabi wurin, da zai kunshi tarihin Imam Sadiq (AS) taron zai samu halartar musulmi daga dukkanin bangarorinsu da ke kasar ta Birtaniya. 471904



captcha