IQNA

Faransa Za Ta Saka Tsarin Bayar Da Bashin Baki Na Musulunci

11:48 - October 01, 2009
Lambar Labari: 1832126
Bangaren kasa da kasa; Ma'aikatar kula da harkokin tattalin arziki ta kasar faransa ta sanar cewa za a saka tsarin bayar da bashin banki irin na muslunci a wasu bankunan kasar da nufin jawo hankalin musulmi masu saka hannayen jari.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto; Ma'aikatar kula da harkokin tattalin arziki ta kasar faransa ta sanar cewa za a saka tsarin bayar da bashin banki irin na muslunci a wasu bankunan kasar da nufin jawo hankalin musulmi masu saka hannayen jari.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan wani shiri ne da Faransa ta bullo da shi da nufin jawo hankalin musulmi 'yan kasuwa daga kasashen musulmi daban-daban, wanda hakan zai karfafa tattalin arzikinta, musamman ta fuskar saka hannayen jari a bankunan gwamnati. 471968


captcha