IQNA

Za A Gudanar Da Zaman Taro Kan Harkokin Shari'a A Morocco

11:48 - October 01, 2009
Lambar Labari: 1832127
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi dangane da harkokin shari'a da al'adu da kuma ilimi, wanda cibiyar kula da al'du da ilimin ta kasashen musulmi ISESCO ta dauki nauyin shirya gudanarwa a Morocco.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga daga shafin internet na kungiyar ISESCO cewa; Za a gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi dangane da harkokin shari'a da al'adu da kuma ilimi, wanda cibiyar kula da al'du da ilimin ta kasashen musulmi ISESCO ta dauki nauyin shirya gudanarwa a Morocco.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai samu halartar wakilai daga bangarori daban na kasashen muslmi, inda za su yi nazari a ilmance dangane harkokin shari'a. Daga bisani kuma za a fitar da bayanin bayan taro da zai hada dukkanin mahangar masana kan abubuwan da tarn ya yi dubi a kansu. 471993



captcha