Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na Misrawi cewa; Tsohon piraministan kasar Nrway Kigel Niken ya kirayi kasashen yammacin turai da su canja mummunar siyasarsu ta kyamar addinin muslunci da musulmi.
Ya kuma bayyana hakan ne a lokacin da ake gudanar da wani zama na bincika hanyoyin karfafa tattaunawa tsakanin mabiya addinai a kasar Amurka. Inda ya bayyana cewa babban kuskure ne kasashen yammacin turai suke yi wajen kyamar musulmunci, domin kuwa a cewarsa a ddinin Musulunci da musulmi babu wanda zai iya cewa ba zai tafi tare da su ba. 472032