IQNA

Kyautata Ma Mahaifa A Mahangar Kur'ani Mai Tsarki

Bangaren rahoto. Kyautatawa ga mahaifa na matsayi na musamman a mahangar kur'ani mai tsarki, da hakan kuma yake daya daga cikin wajibai da suka rataya a kan duklkanin musulmi ya yi biyayya ga mahaifansa matukar dai ba ta saba wa ubangiji ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na lardin Khuzestan cewa, Kyautatawa ga mahaifa na matsayi na musamman a mahangar kur'ani mai tsarki, da hakan kuma yake daya daga cikin wajibai da suka rataya a kan duklkanin musulmi ya yi biyayya ga mahaifansa matukar dai ba ta saba wa ubangiji ba. Bayanin ya ci gaba da cewa matsayin iyaye a addinin Musulunci matsayi da ya zama wajibi a kiyaye shi. 469820