IQNA

MDD :Za A Hukumta Shugabannin HKI A Kotun Laifuka

14:43 - October 01, 2009
Lambar Labari: 1832202
Bangaren siyasa;' shugaban majalisar dokokin Iran ya yi nuni da hukumta shugabannnin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a gaban kotun duniya mai binciken manyan laifuka.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: Ali Larjani shugaban majalisar dokokin a zaman majalisar na bainar jama'a ne ya fito karara ya bayyana cewa; komitin bincike na majalisar dinkin duniya yana bincike da nazari kan wuce gonad a irin a da zaluncin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da rashin tausayin da ta nunawa al'ummar yankin Gaza a lokacin yaki na cikin kwanaki ashirin da daya. Har ila yau shugaban majalisar dokokin na Iran ya kara da cewa komitin kare hakkin dan adam ma na majalisar dinkin duniya shi ne ya fara bincike kan wannan inda ya tabbatar da aikata laifukan da ake zargin haramtacciyar kasar Ira'ila da su.

472027

captcha