IQNA

An Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani Mai Tsarki A Jamus

10:39 - October 03, 2009
Lambar Labari: 1832627
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Jamus, wanda kungiyar Turkawa mazauna kasar jamus ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Postgazatesi cewa; An gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Jamus, wanda kungiyar Turkawa mazauna kasar jamus ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka gudanar a kasar ta Jamus tana daya daga cikin muhimman abubuwan da aikce-aikace da kungiyar Turkawa mazauna kasar Jamus ke gabatarwa domin kara wayar da kan mutane dangane da addinin Musulunci, tare da kara karfafa gwiwar musulmin kasar wajen ci gaba da yin riko da koyarwar addinin muslunci.472716






captcha