Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ne bayan ta nakalto daga jaridar Bahrain Al'ausat ta watsa rahoton cewa an girmama wadanda suka shirya gasar karatun kur'ani ta Jalwa bin Dawi . Ita dai wannan gasar ta kasu gida uku .Kashin farko daga Amma zuwa juzi'I na talatin.sai kuma ta yan kasa da shekaru goma zuwa shatakwas da za su hardace juzu'I goma daga suratul Ankabut sai kuma kashi na karshe daga suratul Nasi day a hada manya da kankana babu banbanci illa iyaka hardace kur'ani baki daya.
472684