Bangaren kasa da kasa: A kasar Turkiya ne aka bude cibiyar gudanar da bincike kan Shi'anci inda aka samu halartar ministan ilimi mai zurfi na kasar.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga Zeynebiye ta watsa rahoton cewa: an hude wata cibiya ta bincike da nazari kan shi'anci a jami'ar a kasar Turkiya da kuma dakin ajiyar littafai na Aflul Baiti a wannan kasa har iloa yau kuma za a rika nazari kan matsalolin da ke addabar kasashen musulmi dab a na shi'a ba . A wani taron manema labarai Durmus Bostug shugaban jami'ar ya yi jinjinawa mahukumtan kasar ta Turkiya da suka yi wannan nazari da hangen nesa da zai taimakawa hanyar ilimi da zamantakewar addini a kasar ta Turkiya.
472675