IQNA

Za A Gudanar Da Taron Dar Tauhid Islam A Kasar Faransa

18:18 - October 04, 2009
Lambar Labari: 1833456
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani taron addinin musulunci a kasar Faransa na Dar Tauhid Islam, wanda za a gudanar a yau a birnin Paris fadar mulkin kasar ta Faransa.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa; Za a gudanar da wani taron addinin musulunci a kasar Faransa na Dar Tauhid Islam, wanda za a gudanar a yau a birnin Paris fadar mulkin kasar ta Faransa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar malaman addinin muslunci na kasar ta Faransa da ma wasu daga cikin kasashen turai, gami dam asana daga wasu kasashen larabawa da na musulmi. 472902



captcha