IQNA

Cibiyar Musulunci Ta Kasar Faransa Ta Shirya Gudanar Da Taron Musulunci

14:16 - October 05, 2009
Lambar Labari: 1833791
Bangaren kasa da kasa; Cibiyar kula da harkokin musulmi ta kasar Faransa ta Shirya gudanar da wani taro kan akidar musulunci da tauhidi.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa; Za a gudanar da wani taron addinin musulunci a kasar Faransa na Dar Tauhid Islam, wanda za a gudanar a yau a birnin Paris fadar mulkin kasar ta Faransa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar malaman addinin muslunci na kasar ta Faransa da ma wasu daga cikin kasashen turai, gami dam asana daga wasu kasashen larabawa da na musulmi. Cibiyar kula da harkokin musulmi ta kasar Faransa ita ce ta Shirya gudanar da wannan taro kan akidar musulunci da tauhidi.472932


captcha