Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya cewa; Babban sakataren kungiyar kula da ayyukan kungiyoyin muslmi ta kasa da kasa; Abdullah Muhsen ya sanar cewa za a gudanar da zaman tattaunawa tsakanin mabiya addinai domin kara kusanto da fahimtar juna tsakaninsu. Bayanin ya ci gaba da cewa taron za a gudanar da shi cikin 'yan kwanakin nan domin tattauna hanyoyin da kafofin yada labarai za su iya bayar da gudunmawa wajen hada kan mabiya addinai. 472959