IQNA

Za Gudanar Da Kasuwar Littafen Musulunci A Koweiti

Bangaren kasa da kasa: za a gudanar da kasuwar baje littafen Musulunci a kasar koweiti.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta KIF ta watsa rahoton cewa; A tsawon kwanaki goma sha biyu marubuta da mawallafa daga kasashe daban-daban na duniya za su baje irin littafen da suka rubuta da suka shafi Musulunci da kuma Kur'ani.A lokacin wannan kasuwa duk wani mai bukata yana iya sayen littafin day a burge shi ko kuma CD da aka nadi littafin da makamantan haka.

473296