Bangaren kasa da kasa; Mataimakin ministan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar saudiyya ya bayyana cewa, gasar kur'ani ta kasa da kasa da kasa da za a gudanar a kasar za a rika watsa ta kai tsaye a gidajen radiyon kasar.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Nasij cewa; Mataimakin ministan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar saudiyya ya bayyana cewa, gasar kur'ani ta kasa da kasa da kasa da za a gudanar a kasar za a rika watsa ta kai tsaye a gidajen radiyon kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa gasar za ta bangarorin karatu da kuma harda gami da haradar hadisai da tafsirin kur'ani. Kasashen musulmi da dama ne suke halartar wannan gasa da ake gudanarwa a kowace shekara.474417