Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa; An bude wani babban baje koli na kayayyakin sadarwa na digital a hubbaren Imam Khomeini (RA) da ke kudancin birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shi ne karo na uku da ake gudanar da irin wannan baje koli na kayyakin sadarwa na digital a jamhuriyar musulunci ta Iran. Kamfanoni daga kasashe daban-daban ne suka kawo kayayyakinsu, da suka hada da kasashen yankin gabas ta tsakiya da kuma Asia, da kuma Amurka gami da kasashen kudancin Amurka. 474439