Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga Jodan ta nakalto daga jaridar Aldastur cewa; masu halartar wannan zanga-zangar kin jinin haramtacciyar kasar Isra'ila da yin Allah wadai da mummunan aikinta sun kona tutar haramtacciyar kasar ta Isra'ila da rera bakaken kal;amai na tsinuwa kan shugabannin Haramtacciyar kasar Isra'ila da munanan aikinta .Har ila sun yi kira da babbar murya ga mahukumta da kungiyoyi masu zaman kansa na kasa da kasa da na yankin da su dauki mataki a cikin hamzari na kawo karshen wannan cin zalum da ake nuna wa palasdinawa.
474935