IQNA

Gwagwarmaya Ce Kawai Hanyar Intar Da Palasdinu

13:17 - October 07, 2009
Lambar Labari: 1834776
Bangaren ilimi da tunani: hadin guiwar malummai musulmai a Jabalul Amil a Labanon sun yi nuni da makircin haramtacciyar kasar Isra'ila na mamayewa da killace Masallacin Aksa da cewa hanyar kawo karshen wannan lamari da intar da palasdinu it ace kawai ringumar gwagwarmaya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna daga Labanon ta watsa rahoton cewa: hadin guiwar malummai musulmai a Jabalul Amil a Labanon sun yi nuni da makircin haramtacciyar kasar Isra'ila na mamayewa da killace Masallacin Aksa da cewa hanyar kawo karshen wannan lamari da intar da palasdinu it ace kawai ringumar gwagwarmaya. Har ila yau sun yi kira ga mahukumta da shugabanni na larabawa da na musulmi da su taimakawa kungiyoyi da daidaiku yan gwagwarmaya ta duk hanyar da za su iya domin wannan it ace hanya ta kawo karshen wannan matsala da kumci da al'ummar Palasdinu ke ciki da kuma wanda masallacin kudus ke ciki yau shekaru aru-aru.


474872
captcha