IQNA

Darul Shafa'a Na Imam Sajjad (AS) Ya Ci Gaba Da Kaso Araba'in A Karbala'a

Bangaren siyasa da zamantakewa: shugaban cibiyar bincike ta gamsu da yadda Darul Shafa'a na Imam Sajjad (AS) ya samu ci gaba da kaso arba'in.
A wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ikna ta yi da Muhammad Hasan Asafri shugaban cibiyar ya bayyana cewa a n samu ci gaba a ginin da aka fara na darul Shafa'a a Karbala kuma ya fito fili ya bayyana cewa; wannan gini na darul Shafa'a zai taimaka ko shakka babu wajen inganta kula da lafiya a wannan kasa musamman a yankin Karbala'a na Iraki da ake samu masu ziyara dubbai daga fadin kasar ta Iraki da kuma kasashen duniya musamman na yankin irin su Iran da Suriya da Labanon.


474349