IQNA

Goyan Baya da Taimakawa HKI Da Amerika Da Turai Ke Yi Ba Za Ta Cimma Nasara Ba

14:40 - October 08, 2009
Lambar Labari: 1835087
Bangaren siyasa da zamantakewa;daruruwan matasa a Turkiya ne suka gudanar da zanga-zanga a dandalin Kizilayi na birnin Ankara domin jaddada cewa duk wani goyan baya da taimakawa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da Amerika da Turai ke yi ba zai kai ga cimma nasara ba.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce daga Turkiya bayan ta nakalto daga jaridar Islam Yaum ta watsa rahoton cewa: daruruwan matasa a Turkiya ne suka gudanar da zanga-zanga a dandalin Kizilayi na birnin Ankara domin jaddada cewa duk wani goyan baya da taimakawa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da Amerika da Turai ke yi ba zai kai ga cimma nasara ba. Wannan ba shi ne karon farko a cikin wannan mako da dubban yan kasar Turkiya ke gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma mummunan aikinta.

475663

captcha