Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na ma'iakatar kula da harkokin ayyukan haji a kasar Afganistan cewa; An kafa wani kwamiti da zai kula da ayyukan haji a kasar Afganistan, wanda a jiya ya gudanar da zamansa a karo na takwas. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daya daga cikin muhimman abubuwan da ma'aikakatar ta mayar da hankali kansu domin ganin an gudanar da ayyukan haji na bana lami lafiya.475758