Bangaren kasa da kasa: komitin koli mai sa ido kan gudanar da taron farko kan matsalar kafirta mutane da dalilai da kuma tasirinsu gami da hanyoyin magance matsalar y ace za a gudanar a Saudiya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Nasij cewa: komitin koli mai sa ido kan gudanar da taron farko kan matsalar kafirta mutane da dalilai da kuma tasirinsu gami da hanyoyin magance matsalar y ace za a gudanar a Saudiya. Sa'id Alarabi Alharati shugaban komitin sa idon kan wannan taro da yadda za a gudanar da shi ya bayyana cewa: shugabanni da daman e dam asana da manazarta da kuma kwararru kan ilimin tarbiya da masu kafafen watsa labarai daga kasashen musulmi da sauran na kasashen duniya za su halarci wajen wannan taro da suka bayyana muhimmancinsa musamman a wannan lokaci da yanayi na rayuwar duniya cikin kumci da damuwa.
476176