IQNA

Tawagar Iraniyawa Makaranta Kur'ani Ta Kai Ziyara A Kasar Sudan

16:36 - October 11, 2009
Lambar Labari: 1836225
Bangaren kasa da kasa; Tawagar Iraniyawa makaranta kur'ani ta kai wata ziyara a kasar Sudan idan ta ziyarci cibiyar mabiya darikar Tijjaniya da ke yankin Umdurman da ke kusa da birnin Khartum.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa; Tawagar Iraniyawa makaranta kur'ani ta kai wata ziyara a kasar Sudan idan ta ziyarci cibiyar mabiya darikar Tijjaniya da ke yankin Umdurman da ke kusa da birnin Khartum. Bayanin ya ci da cewa ziyara na daya daga cikin muhimman ayyukan da wannna tawaga ta aiwatar a cikin 'yan lokutannan. Daga bisani kuma wannan tawaga za ta halarci tarukan karatun kur'ani mai tsarki da aka shirya gudanarwa a wasu yankuna na kasar Sudan domin girmama su, tare da basu kyaututtuka da suka hada da kayan a'ada na mutanen kasar Sudan. 476502



captcha