Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin internet na jaridar kasar Saudiyya Albilad cewa; Za a gudanar da taro karo na goma sha biyu a birnn Alkahira na kasar Masar dangane da harkokin kasuwanci na kasashen musulmi, wanda kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa an yi tattaunawa ta musamman dangane da yadda zaman zai gudana tsakanin shugabannin kamfanoni kasashen musulmi, da kuma irin rawar da kamfanonin musulmi za su iya takawa wajen shawo kan matsalar tattalin arziki da ake fama da ita a duniya. 476589