IQNA

A Yau Ne Za A Kammala Gasar Karatun Kur'ani A Saudiyya

16:35 - October 11, 2009
Lambar Labari: 1836234
Bangaren kasa da kasa; A yau ne za a kammala gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Saudiyya ta kasa da kasa da ta kunshi karatun kur'anin da kuma tafsirinsa.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya cewa; A yau ne za a kammala gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Saudiyya ta kasa da kasa da ta kunshi karatun kur'anin da kuma tafsirinsa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa ta samu halartar makaranta daga sassa daban-daban na duniya musamman ma kasashen larabawa da na musulmi. An bayyana sunayen wadanda suka lashe gasar a bangaren tafsiri da kuma karatu gami da harda. 476499


captcha