IQNA

An Bude Baje Kolin Kayayyakin Rubutun Iraniyawa A Sudan

11:33 - October 13, 2009
Lambar Labari: 1837035
Bangaren kasa da kasa; An bude wani baje kolin kayyakin rubutun Iraniyawa a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan, wanda ke samun karbuwa daga al'ummomin kasar daga dukkanin kusurwoyinta.
Kamfanin dillancin labaran Iqn aya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran kasar Sudan cewa; An bude wani baje kolin kayyakin rubutun Iraniyawa a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan, wanda ke samun karbuwa daga al'ummomin kasar daga dukkanin kusurwoyinta. Bayanin ya ci gaba da cewa wasu daga cikin al'ummomin Sudan da suka halarci taron baje kolin sun nuna matukar gamsuwarsu da jin dadinsu dangane da yadda ake gudanar da wannan baje koli. 477752
captcha