Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga daga dan rahoto na musamman da ke tare da tawagar Iraniyawa makaranta kur'ani a Sudan cewa; Shirin kur'ani da aka tattara a cikin fayafai na na'ura mai kwakwalwa sun samu karbuwa a kasar Sudan, bayan da aka nuna shi a masallatai daban-daban na kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan tawaga ta gudanar da ayyuak da dama a fagen ilmomin kur'ani mai tsarki a ziyarar da take kaiwa a kasar ta Sudan, lamrin da ya kayatar ga al'ummar kasar. 478233