Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran kasar Malazia cewa; Za a gudanar da zaman taro a birnin Kualalampour na kasar Malazia domin yin dubi kan matsayin mata da muhimmancinsu a cikin al'umma a mahangar kur'ani mai tsarki. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro ya zo bayan kiran da wasu malamai suka yi da ke neman a kara wayar da kan mata dangane da rawar da za su iya takawa wajen ciyar da al'umma gaba, da kuma ayyukan da suka kebance a cikin rayuwa ta zamantakewa. 478296