Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran WAM na kasar hdaddiyar daular larabawa cewa; Za a gina wani sabon masallaci mai girma a birnin Abu Dabi na kasar Hadaddiyar daular larabawa, wanda aka fitar da surar gininsa a cikin makonnan. Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka an kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata domin gabatar da zanen yadda ginin masallacin zai kasance. 478395