Bangaren fikira da ilimi; An fara gudanar da tarukan tunawa da ranar shahadar imam Sadiq (AS) a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Kabul na kasar Afganistan cewa; An fara gudanar da tarukan tunawa da ranar shahadar imam Sadiq (AS) a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan. Bayanin ya ci gaba da cewa wadannan taruka masu albarka da ake gudanarwa a kasar Afganistan suna samun karbuwa a wajen al'ummar kasar da aka sansu da kishin Musulunci, da hakan ya hada da mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da ma 'yan sunna. 478448