Bangaren kasa da kasa; An zabi birnin najaf Alasharaf na kasar Iraki a matsayin babban birnin duniyar musulmi a shekara ta 2012, wanda ministocin ma'aikatun kula da harkokin al'adu na kasashen musulmi ne amince da hakan a zamansu.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Syria cewa; An zabi birnin najaf Alasharaf na kasar Iraki a matsayin babban birnin duniyar musulmi a shekara ta 2012, wanda ministocin ma'aikatun kula da harkokin al'adu na kasashen musulmi ne amince da hakan a zamansu. Bayanin ya ci gaba da cewa an zabi Najaf ne saboda tsawon tarihi da take da shi a cikin tarihin addinin Musulunci, da kuma rawar da birnin ke takawa ta fuskar yada ilimi. 479061