Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar saudiyya cewa; An fara gudanar da wani baje kolin kayayyakin rubuce-rubucen Musulunci a kasar Saudiyya, da nufin kara fito da fasahar addinin muslunci ta tsawon tarihi. Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka dubban mutane suke halartar wannan baje koli da suka hada da daruruwa da suka zo domin nuna fasahrsu ta rubutun Musulunci. 479148