Bangaren siyasa:komitin al'adu na majalisar dokoki ya fara bincike kan take hakkin dan adam da amerika ke yi a duniya da kuma dayan bangare kan Ranar kudus da matakin gwagwarmayar al'ummar palasdinu a yankin.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; majalisar dokokin Iran musamman komitin da ke kula da al'adu a majalisar ya fara wani nazari kan abubuwa guda biyu na farkonsa kan babakere da cin zalumi da Amerika ke nunawa sauran kasashe sai kuma matsayi na biyu kan ranar Kudus da hanyar gwagwarmaya da al'ummar Palasdinu suka yi riko da ita a kokowar neman hakinsu da suke yi.
479674