Bangaren kasa da kasa; Ma'ikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar saudiyya ta bayar da labarin cewa, za a tarjama kur'ani mai tsarki a cikin harshen ibraniyanci da nufin kara yada addinin musulunci tsakanin masu fahimtar wannan yare.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Muhit na kasar saudiyya cewa; Ma'ikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar saudiyya ta bayar da labarin cewa, za a tarjama kur'ani mai tsarki a cikin harshen ibraniyanci da nufin kara yada addinin musulunci tsakanin masu fahimtar wannan yare. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar yin hakan ita ce kara yada fahimtar addinin musulunci a dukkanin sassa na duniya. 479167