Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin internet na bangaren kula da shirya taruka na kungiyar kula da harkokkin ilmi da al'adu na kasashen musulmi cewa; Za a gudanar da tarukan farfado da tattaunawa tsakanin al'adu musamman ma tsakanin kasashen musulmi a kasar Chadi. Kungiyar ta ISESCO zata dauki nauyin shirya gudanar da wannan taro da zai samu halartar mutane daga sassa daban-daban na duniya. 479323