Kamfanin dillancin labaran Iqn ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran sabah cewa; Shugaban majalisar dokokin kasar Italia ya yi kira da saka darussan addinin Musulunci a cikin manhajar karatu a makarantun kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa shaugaban majalisar dokokn kasar ta Italia ya bukaci dukkanin daraktoci na cibiyoyin ilimi, da kuma shugabannin makarantu, da su saka sa'a daya a cikin mako domin karantar da addinin Musulunci. 480176