Kamfanin dillancin labaran Iqn ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran islam online cewa; Manyan jami'an 'yan sanda na kasar Birtaniya sun kai wata ziyara a masallatan kasar, da nufin ganawa da mabiya addinin Musulunci na kasar wadanda su ne marassa rinjaye a kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan ziyara ta zo a daidai lokacin wasu daga cikin al'ummomin kasar suke ta kara nuna kyamar addinin musuluci da musulmi, sakamakon irin yadda gwamnatin kasar take kallon Musulunci tare da bayyana shi da mummunar sua ga al'ummar kasar.480126