Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Bahrain cewa; An kammala dukkanin shirye-shiryen fara gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Bahrain, wadda za a gudanar a karo na bakwai a wannan shekara. Babban kamfanin na kasar Bahrain Junaid shi ne kan dauki nauyin gudanar da wannan gasa, wadda za ta samu halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daban na kasar.480700