Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na cibiyar kula da harkokin ilmi da al'adu tat a Iran a reshenta dake kasar zambia cewa; Za a gudanar da wani zaman taro a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar haihur Imam Reda (AS) dangane da mahangarsa kan ilmomin da ke tattare a cikin alkur'ani mai tsarki. Bayanin ya ci gaba da cewa za a gudanar da taron ne a babban dakin taruka na birnin Lusaka na kasar zambia. 480343