Kamfanin dillancin labaran Iqna ya zanta da daya daga cikin manyan malaman kasar Iraki Sayyid Munzir Hakim, wanda ya bayyana cewa; Shahid Ayatollah Ozma Sayyid Bakir Sadr ya bayar da gagarumar gudunmawa ta fuskacin karfafa tattalin arzikin Musulunci a ilmance a cikin rubuce-rubucensa. Ya ci gaba da cewa shahid Sadr mutum ne da duniya ta yi kewarsa ta fuskoki da dama, ba ma wai kawai ta fuskacin ilmantarwarsa ta addini ba, a'a har ma ta fuskacin ilmantarwa a fagagen siyasa da tattalin arziki.480861