IQNA

14:47 - October 24, 2009
Lambar Labari: 1840982

An Bude Bankin Musulunci A Karon Farko A Kasar Tunisia

Bangaren kasa da kasa; A karon farko an bude bankin musulunci a kasar Tunisia wanda aka sanya wa suna zaitunah, wanda ya fara da hannun jari da ya kai dalar Amurka miliyan ashirin da biyar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Faransa cewa; A karon farko an bude bankin musulunci a kasar Tunisia wanda aka sanya wa suna zaitunah, wanda ya farad a hannun jari da ya kai dalar Amurka miliyan ashirin da biyar. Wannan banki zai mayar da hankali ne wajen kara bunkasa harkokin kudi da ajiyar bankuna bisa ka'idoji irin na addinin muslunci. Yanzu haka dai bankin ya fara gudanar da ayyukansa da kudaden da suka fara shiga cikinsa daga musulmin kasar. 482660


captcha