IQNA

An Sanar Da Sunayen Wadanda Suka Lashe Kyautar Hidimar Kur'ani

19:49 - October 25, 2009
Lambar Labari: 1841530
Bangaren kasa da kasa; An sanar da sunayen wadanda suka lashe kyautar ban girma ta matasa masu hidima ga kur'ani mai tsarki, wadda gwamnatin kasar Bahrain ta kebance domin karfafa gwiwar matasa kan harkokin kur'ani.
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dilalncin labaran kasar Bahrain cewa; An sanar da sunayen wadanda suka lashe kyautar ban girma ta matasa masu hidima ga kur'ani mai tsarki, wadda gwamnatin kasar Bahrain ta kebance domin karfafa gwiwar matasa kan harkokin kur'ani. Bayanin ya ci gaba da cewa wadanda suka karbi wannan kyauta dukakninsu matasa 'yan asalin kasar, an kuma zanta da su a kafofin yada labarai daban-daban na kasar da wajenta. 482916



captcha