Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin post cewa Ofishin magajin garin birnin Nordestedt na kasar Jamus ya bayar da izini ga musulmin birnin da su gina wata makabarta ta musulmi domin rufe mabiya addinin musulunci da suka rasu. Bayanin ya ci gaba da cewa tun a lokutan baya ne kungiyoyin musulmi na kasar Jamus suka fara neman da a ba su damar gina makbartunsu domin bizne musulmi wadanda suka rasa rayukansu, daga bisani kuma aka amsa kiran nasu.485498