Kamfanin dillancin labaran Iqna ya na kalto daga shafin internet na MAP cewa; An bude wata makarantar koyar da karatun kur'ani mai tsarki a birnin Imam Nafiya na kasar Morocco, da za ta rika koyar da kanan yara karatu da ilmomin kur'ani mai tsarki. Bayanin ya ci gaba da cewa an gabatar da shirin bude wannan makaranta tun a cikin shekarun da suka gabata, amma aiwatar da shirin ginin ya samu tsaiko na wasu 'yan shekaru, ka na daga bisani aka fara aiwatar da shi kamar yadda aka shirya tun farko.485398