IQNA

Malaman Addini A Iraki Sun Haramta Yin Amfani Da Addini Don Zabe

9:47 - November 01, 2009
Lambar Labari: 1843165
Bangaren kasa kasa; Manyan malaman addini a birnin Najaf Ashraf ta kasar Iraki sun haramta yin amfani da addini domin cimma burinsu na zabe.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Aswatul Iraki cewa; Manyan malaman addini a birnin Najaf Ashraf ta kasar Iraki sun haramta yin amfani da addini domin cimma burinsu na zabe. Bayanin ya ci gaba da cewa babu wani dalili da zai sanya mai neman takara ya yi amfani da addini domin kawai ya cimma burinsa na siyasa. 485373



captcha