Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na islam online cewa; Za a fara aiwatar da wani shiri na koyar da harshen larabci a makarantun kasar Ukraine, inda yanzu haka makaratun kasar 45 ne suka amince su fara aiwatar da wannan shiri. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri an gabatar da shi ne tun lokutan baya, amma yanzu haka ana gab da fara aiwatar da shi a makarantu da dama na kasar. Babbar manufar shirin ita ce bayar da dama ga yara su koyi harshen domin sanin abin da aka rubuta a cikin wannan harshe domin amfaninsu. 485552