IQNA

Dukkanin Ayyukan Fasaha Na Nuni Ne Da Baiwa Ta Musamman

Bangaren Fasaha; Dukkanin ayyukan fasaha da ke akwai a cikin duniya wata manuniya ce kan wata baiwa ta musumman da ta kebanci ma'abuta wannan fasaha.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Iqna da daya daga cikin wasu masu fasaha na kasar Iran Babak Haidari ya bayyana cewa; Dukkanin ayyukan fasaha da ke akwai a cikin duniya wata manuniya ce kan wata baiwa ta musumman da ta kebanci ma'abuta wannan fasaha. Ya ci gaba da cewa kowace irin fasaha da za a iya gani daga wani mutum to ko shakka babu wannan wata baiwa ce gare shi daga ubangiji. Amma ba ko da yaushe ne mutum yak an yi amfani da baiwar da ubangiji ya ba shi ba domin gudanar da ayyuka da suka dace. 485604