IQNA

Za A Gudanar Da Tarukan Kan Harkokin Kudi A Musulunci

17:50 - November 02, 2009
Lambar Labari: 1843888
Bangaren siyasa da zamantakewa; Za a gudanar da wani zaman taro kan harkokin kudi a mahangar addinin musulunci, wanda kuma wannan shi ne karo na biyu da za a gudanar da irin wannan taro.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa; Za a gudanar da wani zaman taro kan harkokin kudi a mahangar addinin musulunci, wanda kuma wannan shi ne karo na biyu da za a gudanar da irin wannan taro. Bayanin ya ci gaba da cewa za a gudanar da taron ne a jami'ar Mofid da ke birnin Qom a jamhuriyar musulunci ta Iran, wanda zai samu halartar jami'ai daga sssa daban-daban na kasashen musulmi, da kuma masana kan harkokin kudi. 485908

captcha